Acts 7

Jawabin Istifanus Ga Majalisa

1Sai babban firist ya tambaye shi ya ce, “Waɗannan zargen gaskiya ne?”

2Game da wannan ya amsa, ya ce: “ʼYanʼuwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran. 3Allah ya ce, ‘Ka bar ƙasarka da kuma mutanenka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.’
Far 12.1


4“Saboda haka ya bar ƙasar Kaldiyawa ya kuma yi zama a Haran. Bayan mutuwar mahaifinsa, Allah ya aikar da shi wannan ƙasar da yanzu kuke zama. 5Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro. 6Allah ya yi magana da shi ta haka: ‘Zuriyarka za su yi baƙunci a wata ƙasar da ba tasu ba, za su yi bauta su kuma sha wulaƙanci har shekara ɗari huɗu. 7Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’
Far 15.13, 14
8Saʼan nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan.

9“Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi 10ya kuma cece shi daga dukan wahalolinsa. Ya ba wa Yusuf hikima ya kuma sa ya sami farin jini a wurin Firʼauna, sarkin Masar; saboda haka ya mai da shi mai mulki a kan Masar da kuma dukan fadarsa.

11“Sai yunwa ta auko wa dukan Masar da Kanʼana, ta kawo wahala mai tsanani, kakanninmu ba su iya samun abinci ba. 12Saʼad da Yaƙub ya ji cewa akwai hatsi a Masar, sai ya aiki kakanninmu ziyararsu ta farko. 13A ziyararsu ta biyu, Yusuf ya faɗa wa ʼyanʼuwansa wane ne shi, Firʼauna kuwa ya sami sani game da iyalin Yusuf. 14Bayan wannan, Yusuf ya aika a zo da mahaifinsa Yaƙub da dukan iyalinsa, gaba ɗaya dai mutum sabaʼin da biyar ne. 15Sai Yaƙub ya gangara zuwa Masar, inda shi da kuma kakanninmu suka mutu. 16Aka dawo da gawawwakinsu Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya daga wurin ʼyaʼyan Hamor da waɗansu kuɗi a Shekem.

17“Da lokaci ya yi kusa da Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim, sai yawan mutanenmu da suke a Masar ya ƙaru ƙwarai. 18Saʼan nan wani sarki, wanda bai san kome game da Yusuf ba, ya zama mai mulkin Masar. 19Ya kuwa wulaƙanta mutanenmu sosai, ya kuma gwada wa kakanni-kakanninmu azaba ta wurin tilasta su su zubar da sababbin jariransu, don su mutu.

20“A lokacin nan aka haifi Musa, shi kuwa ba kamar sauran jarirai ba ne. Wata uku aka yi renonsa a gidan mahaifinsa. 21Saʼad da aka ajiye shi a waje, diyar Firʼauna ta ɗauke shi ta kuma rene shi kamar ɗanta. 22Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka.

23“Da Musa ya cika shekara arbaʼin da haihuwa, sai ya yanke shawara yǎ ziyarci ʼyanʼuwansa Israʼilawa. 24Ya ga ɗayansu yana shan wulaƙanci a hannun wani mutumin Masar, sai ya je ya kāre shi, ya rama masa ta wurin kashe mutumin Masar ɗin. 25Musa ya yi tsammani mutanensa za su gane cewa, Allah yana amfani da shi don ya cece su, amma ba su gane ba. 26Washegari, Musa ya sadu da Israʼilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku ʼyanʼuwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’

27“Amma mutumin da yake wulaƙanta ɗayan, ya tura Musa a gefe ya ce, ‘Wa ya mai da kai mai mulki, da alƙali a kanmu? 28Kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan na jiya?’
Fit 2.14
29Saʼad da Musa ya ji haka, sai ya gudu zuwa ƙasar Midiyan, inda ya yi baƙunci, ya kuma haifi ʼyaʼya biyu maza.

30“Bayan shekaru arbaʼin suka wuce, sai malaʼika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai. 31Saʼad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce: 32‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’
Fit 3.6
Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.

33“Saʼan nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne. 34Hakika na ga wulaƙancin da ake yi wa mutanena a Masar. Na ji nishinsu na kuma sauka domin in ʼyantar da su. Yanzu ka zo, zan aike ka ka koma Masar.’
Fit 3.5, 7, 8, 10


35“Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin malaʼikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yǎ zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu. 36Ya fitar da su daga Masar ya kuma yi ayyukan da abubuwan banmamaki a Masar, a Jan Teku, da kuma cikin hamada har shekara arbaʼin.

37“Wannan Musa ne ya faɗa wa Israʼilawa cewa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’
M Sh 18.15
38Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da malaʼikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don ya miƙa mana.

39“Amma kakanninmu suka ƙi yin masa biyayya. A maimakon haka, sai suka ƙi shi a cikin zuciyarsu kuwa suka koma Masar. 40Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar-ba mu san abin da ya faru da shi ba!’
Fit 32.1
41A lokacin ne suka ƙera gunki mai siffar ɗan maraƙi. Suka kawo masa hadayu suka kuma yi bikin girmama abin da suka ƙera da hannuwansu. 42Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa, cewa:

“ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki
shekaru arbaʼin cikin, hamada, Ya gidan Israʼila?
43Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek,
da tauraron allahnku Refan,
gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.
Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’
Amos 5.25
gaba da Babilon.
44“Kakanni-kakanninmu suna da Wuri mai tsarki na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani. 45Bayan sun gāji Wuri mai tsarkin nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga alʼumman da Allah ya kora a idanunsu. Wuri mai tsarki ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda, 46wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yǎ yi wa Allah na Yaƙub wurin zama. 47Amma Solomon ne ya gina masa gida.

48“Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa:

49“ ‘Sama ne kursiyina,
duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata.
Wane irin gida za ka gina mini?
Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance?
In ji Ubangiji.
50Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’
Ish 66. 2

51“Ku mutane masu taurin kai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku: Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki! 52An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi—  53ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin malaʼiku amma ba ku yi biyayya da ita ba.”

Jifan Istifanus

54Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu. 55Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah. 56Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”

57Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya. 58Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.

59Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi adduʼa ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” 60Saʼan nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.

Copyright information for HauSRK